Gwamnatin Tarayya ta ce za ta tura masu bautar kasa 300 zuwa cibiyoyin sauya motocin man fetur zuwa amfani da iskar gas, bayan sun kammala daukar horo tare da samun takardar shaidar zama kwararrun masu aikin CNG.
Babbar Mataimakiyar Shugaban Kasa kan shirye-shiryen matasa, sa ido da aiwatar da manufofi, Dakta Titilope Badamosi, ce ta bayyana hakan yayin kaddamar da shirin horas da 'yan bautar kasa kan sauya motocin daga fetur zuwa amfani da gas din CNG a sansanin NYSC da ke Kubwa, Abuja.
Badamosi ta ce za a gudanar da shirin a dukkan shiyyoyin siyasar kasar nan guda shida, kuma yana daga cikin matakan da gwamnati ke dauka domin bai wa matasa damar taka muhimmiyar rawa wajen sauya tsarin amfani da makamashi.
Ta ce shirin na da burin sauya motoci
100,000 daga fetur zuwa CNG a kowace shekara, yayın da masu hidimar kasa 300 za su samu horo da takardar shaidar kwarewa sannan a tura su cibiyoyin CNG daban-daban.
Ministan Matasa, Ayodele Olawande, ya ce horon zai samar da karin damar aikin yi da kuma bunkasa sana'o'in matasa bayan kammala bautar kasa.
A nasa bangaren, Darakta-Janar na
NYSC, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ya ce shirin ya nuna hadin gwiwar hukumomin gwamnati wajen tallafa wa shirin sauya makamashi na Najeriya, yana mai cewa NYSC ta horar da sama da 'yan bautar kasa miliyan uku a fannoni daban-daban tun daga shekarar 2012 zuwa yau.