Aƙalla mutum 37 ne aka ruwaito sun mutu bayan sun shaƙi hayaƙi mai guba yayin da ake zargin wasu mutane da satar man fetur a wani wurin sauke kaya na jiragen ruwa a Jihar Ribas.

Lamarin ya faru ne a daren Alhamis a Okari Jetty, da ke yankin Okrika, inda ake zargin wasu matasa daga Okrika da ƙauyukan da ke makwabtaka da yankin sun taru domin kwashe man fetur daga wani wurin da aka yi wa bututun mai ƙulli ba bisa ƙa'ida ba.

Rahotanni sun ce fiye da mutum 100 ne suka isa wurin da ƙananan kwale-kwale, yayin da wani jirgin ruwa ke loda man fetur a yankin.

An ce matsalar ta fara ne bayan wani ƙamshi mai ƙarfi ya bazu a wurin, lamarin da ya sa mutane da dama suka fara faɗuwa, yayin da wasu suka faɗa cikin ruwa.

Ƙungiyar Youths and Environmental Advocacy Centre, YEAC-Nigeria, ta tabbatar da mutuwar aƙalla mutane 37, tana mai cewa wasu da dama har yanzu ba a san inda suke ba.

Sai dai rundunar ’yan sandan Jihar Ribas ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta ce ba ta da adadin mutanen da suka mutu a hukumance, inda ta bayyana cewa ana ci gaba da bincike domin gano ainihin abin da ya faru.

Wani kwamandan Civilian JTF a Okrika ya bayar da wata siga, inda ya ce wasu daga cikin mutanen sun je ne domin kwashe man fetur da ya malale a cikin ruwa, kafin hayaƙin da ya fito daga aikin lodin mai ya shafe su.

Lamarin ya sake jawo hankali kan haɗarin satar mai da lalata bututun mai a yankin Neja Delta, musamman ga matasan da ke shiga irin waɗannan ayyuka saboda rashin aikin yi da matsin tattalin arziki.