Kafofin yaɗa labarai na Koriya ta Kudu sun ruwaito cewa gwamnatin ƙasar na shirin tura sojoji da kayan aiki domin tallafawa abin da ta kira “’yancin zirga-zirga a mashigin Hormuz”, tare da fara aikin kafin ƙarshen wannan shekara.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito a ranar Alhamis, 3 ga Satumba, cewa majiyoyin gwamnati da na soja sun ce Seoul na ɗaukar matakan doka domin samun amincewar majalisar dokoki kan tura sojojin.

Rahotannin sun ce an riga an tattauna shirin a wani taron majalisar ministoci, yayin da ake shirin gabatar da buƙatar amincewa a hukumance ga majalisar dokokin ƙasar a cikin watan Satumba.

Shirin na zuwa ne a daidai lokacin da matsalolin tsaro a mashigin Hormuz suka ƙaru, musamman hare-haren da ake kai wa jiragen kasuwanci a yankin cikin makonnin baya-bayan nan.

Mashigin Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin safarar makamashi a duniya, lamarin da ya sa ƙasashe da dama ke nazarin matakan da za su ɗauka domin kare zirga-zirgar jiragen ruwa da jigilar kayayyaki ta wannan hanya.

Sai dai kawo yanzu, gwamnatin Koriya ta Kudu ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance da ke tabbatar da shirin tura sojojin ba.