Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya ayyana Juma’a, 14 ga Agustan 2026, a matsayin ranar hutun aiki ga ma’aikatan gwamnati a faɗin jihar, gabanin zaɓen gwamna da za a gudanar ranar Asabar.


Shugaban Ma’aikatan Jihar, Elder Ayanleye Aina, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Olawale Rasheed, ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba.


A cewar sanarwar, an ɗauki matakin ne domin bai wa ma’aikatan da ke buƙatar yin tafiya damar komawa yankunansu, tare da ba su damar shirya yadda za su kaɗa ƙuri’a a zaɓen.


Sai dai, ma’aikatan da ke gudanar da ayyukan gaggawa da muhimman ayyukan gwamnati ba sa cikin waɗanda hutun ya shafa.


Gwamna Adeleke ya kuma yi kira ga ma’aikatan gwamnati, ’yan uwansu da abokansu da su fito domin kaɗa ƙuri’a, tare da kare ƙuri’unsu daga duk wani yunƙurin yin magudi yayin zaɓen.