Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi gargadin cewa annobar Ebola da ke ci gaba da yaɗuwa a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (DRC) na iya zarce annobar da ta fi muni a tarihin cutar, wadda ta auku a Yammacin Afirka tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016.

Annobar Yammacin Afirka ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum 11,000, yayin da WHO ta ce ta yanzu a DRC ta zama annobar Ebola mafi saurin yaɗuwa da aka taɓa gani.

Rahotannin baya-bayan nan sun nuna cewa ya zuwa 11 ga Agusta 2026, Ebola ta kashe mutane 2,011, yayin da adadin waɗanda suka kamu da cutar ya kai 4,381 a larduna biyar na DRC. Annobar ta samo asali ne daga nau'in Bundibugyo na kwayar Ebola, wanda a halin yanzu babu ingantacciyar allurar rigakafi ko maganin da aka amince da amfani da shi a kai.

Dr. Tedros ya ce ma’aikatan lafiya na ci gaba da ƙoƙarin dakile cutar, amma yaƙin da ake yi da ita na fuskantar ƙalubale da suka haɗa da rikice-rikice, ƙarancin kayan aiki da kuma cikas ga kai agajin lafiya ga al’ummomin da abin ya shafa.

A halin yanzu, an fara gwajin asibiti na matakin farko kan alluran rigakafi guda biyu da ake sa ran za su taimaka wajen dakile nau'in Bundibugyo. WHO ta kuma ce ana shirin gwada wata allurar Ebola da ake da ita bisa sakamakon gwaje-gwajen da aka yi kan dabbobi.

WHO ta bayyana cewa saurin yaɗuwar cutar na ƙara zama abin damuwa, musamman ganin cewa wasu daga cikin sabbin kamuwa da cutar ba a iya gano hanyar da suka bi wajen hulɗa da waɗanda suka kamu da ita.