Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta gano gawarwaki tara a kan hanyar Wawa-Lumma da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja, lamarin da ake zargin ’yan bindiga ne suka aikata.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar wa BBC cewa jami’an ’yan sanda da sojoji sun isa wurin bayan samun rahoton gano gawarwakin a ranar Talata.

Ya ce jami’an tsaron sun kwashe gawarwakin daga wurin, yayin da suka ƙara tsaurara sintiri da binciken wuraren da ake zargin ’yan bindiga na fakewa.

SP Abiodun ya bayyana cewa an ƙara yawan jami’an tsaro a kan hanyar Wawa-Lumma da yankunan da ke kewaye da ita, domin hana sake faruwar irin wannan hari da kuma tabbatar da tsaron matafiya.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a wasu sassan Jihar Neja, musamman yadda matafiya ke fuskantar barazanar hare-haren ’yan bindiga.

Hanyar Wawa-Lumma na daga cikin hanyoyin da ke haɗa wasu yankunan jihar, yayin da hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan Neja suka jefa matafiya da mazauna yankunan cikin fargaba.

Rundunar ’Yan Sandan ta ce ayyukan jami’an tsaro na ci gaba da gudana a yankin domin gano waɗanda ke da hannu a kisan tare da tabbatar da cikakken tsaro a hanyar.