Kakakin Fadar White House ta Amurka, Karoline Leavitt, za ta ajiye mukaminta a ƙarshen wannan wata, kamar yadda Shugaba Donald Trump ya sanar.

Trump ya bayyana Leavitt, wadda yake kira ɗaya daga cikin mataimakan da ya fi amincewa da su, ta yanke shawarar barin aikin domin samun ƙarin lokaci tare da ’ya’yanta da sauran iyalinta.

Shugaban ya ce ya fahimci matakin da ta ɗauka kuma yana mutunta shawarar da ta yanke.

Trump ya ƙara da cewa Leavitt za ta ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan masu ba shi shawara a wajen gwamnati, tare da taka rawa a harkokin Jam’iyyar Republican.

Leavitt, mai shekaru 28, ta fara riƙe mukamin Kakakin Fadar White House a bara, inda ta zama mace mafi ƙanƙanta shekaru da ta taɓa riƙe wannan matsayi.

Har yanzu ba a bayyana wanda zai maye gurbin Leavitt ba.

Leavitt ta haifi ’yarta ta biyu a watan Mayu tare da mijinta, Nicholas Riccio, kuma tana da ɗa mai shekaru biyu.

Ta koma bakin aiki a watan da ya gabata bayan kammala hutun haihuwa.

Bayan sanarwar Trump, Leavitt ta rubuta a shafinta na X cewa riƙe mukamin Kakakin Fadar White House ya kasance mata “abin girmamawa da kuma babbar dama ta rayuwa.”