Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙungiyar Manoman Najeriya (AFAN), Shehu Bello, ya ce matsalar da harkar noma a Najeriya ke fuskanta ba wai ƙarancin kuɗaɗen tallafi ba ce, sai dai ƙalubalen gano waɗanda suka cancanci tallafin, samun damar karɓar kuɗin da kuma dawo da lamunin noma.

Bello ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin “Good Morning Nigeria” na gidan talabijin na ƙasa, NTA, kan batun “Cike Gibin Tallafin Noma a Najeriya.”

Ya ce akwai hanyoyi da dama na samar da kuɗaɗe ga harkar noma, amma babban ƙalubalen shi ne yadda za a tabbatar da cewa kuɗin sun isa hannun manoman da suka dace, tare da samar da ingantaccen tsarin dawo da lamunin da aka bayar.

Ya ƙara da cewa magance waɗannan ƙalubale zai taimaka wajen ƙarfafa harkar noma da kuma inganta samar da abinci a Najeriya.