Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta buƙaci matasan Najeriya da su ƙara himma wajen neman ilimi, ƙirƙire-ƙirƙire, kasuwanci da kishin ƙasa domin cimma burinsu da kuma bayar da gudummawa wajen ci gaban ƙasar.
Ta bayyana hakan ne a cikin saƙonta na bikin Ranar Matasa ta Duniya ta 2026, wanda aka gudanar a ranar Laraba, 12 ga Agusta, ƙarƙashin taken “Yanayi Mabambanta, Buri Guda.”
Oluremi Tinubu ta ce duk da bambance-bambancen yanayin rayuwa da ƙalubalen da matasa ke fuskanta, suna da buri iri ɗaya na samun ingantaccen ilimi da kuma damar samun ayyukan yi.
Ta ƙarfafa matasan da su kasance masu himma da jajircewa wajen aiki, tare da amfani da damarmakin da suke da su domin cimma burinsu da kuma taimakawa wajen gina Najeriya mai zaman lafiya da wadata.