Hukumar Kula da Tsaftar Muhalli ta Jihar Kano, REMASAB, ta kai ziyarar aiki ga masu riƙe da sarautun gargajiya a yankin Sabon Gari da ke Ƙaramar Hukumar Fagge, domin ƙarfafa haɗin gwiwa wajen tabbatar da tsaftar muhalli.

Ziyarar ta mayar da hankali ne kan hanyoyin da za a inganta tare da dorewar tsaftar muhalli a yankin Sabon Gari, wanda ke da yawan al’umma da kuma manyan kasuwanni.

A nasa jawabin, Mai Martaba Igwe Dokta Boniface Ibekwe, shugaban al’ummar Igbo mazauna ƙasashen waje, tare da sauran masu riƙe da sarautun gargajiya, sun miƙa godiyarsu ga REMASAB bisa wannan yunƙuri.

Sun kuma tabbatar da cewa za su bayar da cikakken goyon baya ga hukumar domin tabbatar da tsaftar muhalli da kuma kyautata muhalli a yankin.