Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranci manyan jami’an tsaro daga Najeriya zuwa birnin Washington, D.C., domin halartar babban taron Ƙungiyar Aiki ta Haɗin Gwiwa Najeriya da Amurka kan harkokin tsaro.

Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan ƙarfafa haɗin gwiwar yaƙi da ta’addanci, duba ci gaban da aka samu zuwa yanzu, da kuma gano sabbin hanyoyin da za a zurfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.

Daga cikin manyan jami’an tsaron Najeriya da ke cikin tawagar akwai Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Tunji Disu.

Ana sa ran tattaunawar za ta ƙara inganta musayar bayanan sirri, haɗin gwiwar yaki da ta’addanci da kuma sauran ƙalubalen tsaro da ƙasashen biyu ke fuskanta.