Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare ta Jihar Kano ta fara wani taron kwanaki biyu domin ci gaba da tsara kasafin kuɗin jihar na shekarun 2027 zuwa 2029.
Taron na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka wajen inganta tsarin tsara manufofi da kuma gudanar da harkokin kuɗaɗen gwamnati yadda ya kamata.
Daga cikin manyan mahalarta taron akwai Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Isma’il Falgore, da sauran ‘yan majalisar, da Sakataren Gwamnatin Jihar, da kwamishinoni, shugabannin hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.
A jawabinsa, Kwamishinan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare na Jihar Kano, Musa Sulaiman Shanono, ya yi wa mahalarta taron fatan alheri, tare da bayyana fatansa na ganin an cimma manufofin da aka tsara na taron.
Taron zai mayar da hankali ne kan tattauna hasashen kuɗaɗen shiga da jihar ke sa ran samu, da kuma buƙatun ma’aikatu da hukumomin gwamnati.
Haka kuma, za a duba yadda za a daidaita buƙatun ma’aikatu da hukumomi da abin da gwamnatin jihar za ta iya samu a cikin shekaru ukun da ke tafe.
Ana sa ran sakamakon taron zai taimaka wajen samar da kasafin kuɗi mai inganci wanda zai dace da manufofi da shirye-shiryen ci gaban Jihar Kano na shekarun 2027–2029.