Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Ƙasa (NHRC) ta nuna damuwa kan yawaitar kalaman ƙiyayya, kalaman tsokana, barazanar tashin hankali da kuma tsoratar da masu kaɗa ƙuri’a gabanin zaɓen gwamna da za a gudanar a Jihar Osun, da kuma babban zaɓen shekarar 2027.

A yayin wani taron manema labarai a Abuja, Sakataren Hukumar, Tony Ojukwu, ya jaddada buƙatar hukumomin da abin ya shafa su ɗauki matakin gaggawa domin dakile kalaman da ka iya ƙara tayar da hankali tare da kawo cikas ga gudanar da zaɓe cikin lumana.

NHRC ta musamman ja hankalin jama’a kan wasu kalamai masu rarrabuwar kai da ake dangantawa da wasu ’yan Najeriya dangane da zaɓen Jihar Osun.

Hukumar ta buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe da su kasance masu natsuwa da haƙuri, tare da yaɗa saƙonnin da ke ƙarfafa zaman lafiya, juriya da kuma shiga harkokin dimokuraɗiyya.

Haka kuma, hukumar ta yi kira ga ’yan siyasa, shugabannin addinai, magoya bayan jam’iyyu da kafafen yaɗa labarai da su guji amfani da kalaman tsokana ko tayar da hankali, tare da mutunta haƙƙin dukkan ’yan ƙasa yayin da Najeriya ke tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.