Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana Juma’a, 14 ga Agusta, 2026, a matsayin ranar farko ta watan Rabi’ul Awwal 1448 AH.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Wazirin Sakkwato kuma Shugaban Kwamitin Shawara kan Harkokin Addini na Majalisar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya fitar.
Sanarwar ta ce Kwamitin Shawara kan Harkokin Addini na Majalisar Sarkin Musulmi, tare da haɗin gwiwar Kwamitin Ƙasa na Binciken Jinjirin Wata, sun karɓi rahotanni daga kwamitocin ganin wata daban-daban a faɗin ƙasar, waɗanda suka tabbatar da ganin jinjirin watan Rabi’ul Awwal 1448 AH a ranar Alhamis, 13 ga Agusta, 2026, wadda ta kasance ranar 29 ga watan Safar 1448 AH.
Sanarwar ta ƙara da cewa Sultan ya amince da rahotannin da kwamitocin ganin watan suka gabatar, sannan ya ayyana Juma’a, 14 ga Agusta, 2026, a matsayin ranar farko ta watan Rabi’ul Awwal 1448 AH.
Wannan yana nufin cewa Jumma’a ce 1 ga Rabi’ul Awwal 1448 AH a Najeriya.