Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Najeriya ta musanta wani sanarwar bogi da ke yawo a kafafen sada zumunta da manhajojin aika saƙonni, wadda ke ikirarin cewa an dakatar da aikin ɗaukar sabbin ma’aikata na Civil Defence, Correctional, Fire and Immigration Services Board (CDCFIB).
A cikin wata sanarwa, Sakatariyar dindindin ta Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dr. Magdalene Ajani, ta ce takardar mai kwanan wata 11 ga Agusta, mai taken “CDCFIB Recruitment Update”, an jingina ta ne ƙarya ga Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, kuma ba ta fito daga ma’aikatar, ofishin ministan ko CDCFIB ba.
Ma’aikatar ta bayyana cewa takardar bogi ce, tana mai jaddada cewa ministan bai sanya hannu a kanta ba kuma bai fitar da ita ba.
Ta kuma bayyana cewa babu wata shawarar da aka yanke na dage aikin ɗaukar ma’aikatan har zuwa bayan babban zaɓen shekarar 2027.
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta tabbatar da cewa aikin ɗaukar ma’aikatan CDCFIB yana ci gaba, tare da kira ga masu neman aikin da sauran jama’a da su yi watsi da sanarwar bogin.
Ma’aikatar ta shawarci masu neman aikin da su riƙa dogaro da bayanan da ake wallafawa ta shafukan hukuma da aka tabbatar na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da CDCFIB, ciki har da tashar neman aikin da aka amince da ita.