Gwamnatin Tarayya ta ce za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da abokan hulɗa domin inganta kiwon lafiya da tallafa wa ’yan Najeriya masu rauni, musamman mutanen da ke rayuwa da nakasa.
Ministan da ke Kula da Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai al’ummar Karon Majigi da ke kan titin Airport Road a Abuja, inda ya duba yanayin rayuwa da buƙatun kiwon lafiya na mutanen da ke da nakasa.
Daga cikin mutanen da ya ziyarta akwai masu matsalar gani, waɗanda aka yanke wa gaɓoɓi, da mutanen da cutar shan inna da kuturta ta shafa.
Ministan ya kuma amince da gudunmawar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, wadda ta ja hankalinsa kan al’ummar da kuma ƙalubalen da suke fuskanta.
Farfesa Pate ya yaba wa Tulsi Chanrai Foundation bisa ƙoƙarinta na dawo da ganin mutanen da matsalar makanta da za a iya karewa ta shafa.
Ya ce wasu daga cikin waɗanda suka amfana da shirin sun yi nasarar samun tiyata, inda suka sake samun damar gani a karon farko bayan sun rasa gani.
Ministan ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta tattauna da Gwamnatin Babban Birnin Tarayya (FCT) kan buƙatun ilimi da samar da ingantaccen kiwon lafiya na matakin farko ga al’ummar.
Haka kuma, gwamnati za ta duba hanyoyin faɗaɗa tsarin inshorar lafiya domin ya shafi mutane masu nakasa da sauran masu rauni.