Kwamitin Aiki na Shugaban Ƙasa kan Dokar ‘Yan Sanda ta Ƙasa (National Policing Bill) ya ƙara wa’adin miƙa takardun ra’ayoyi da matsaya (memoranda and position papers) kan dokar zuwa Juma’a, 21 ga Agusta, 2026, da ƙarfe 5:00 na yamma agogon Najeriya.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Aiki kan Dokar ‘Yan Sanda ta Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya ce an ƙara wa’adin ne domin bai wa masu ruwa da tsaki ƙarin lokaci su shirya sosai tare da gabatar da ingantattun shawarwari kan dokar.
Kwamitin ya ce yana da ƙudurin tabbatar da cewa tsarin samar da dokar ya ƙunshi tattaunawa mai faɗi da kuma ra’ayoyin ’yan Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki.
Kwamitin ya ce saboda muhimmancin garambawul ɗin ga makomar aikin ’yan sanda da tsaron cikin gida, ya ga ya dace a bai wa masu ruwa da tsaki ƙarin damar gabatar da shawarwari masu ma’ana da ƙwarewa.
Ya ƙarfafa gwiwar lauyoyi, ƙungiyoyin fararen hula, ƙwararrun fannin tsaro, gwamnatocin jihohi, ƙungiyoyin ƙwararru, malamai da masana, da sauran masu sha’awar harkar da su yi amfani da wannan ƙarin lokaci wajen miƙa ra’ayoyinsu.
Sanarwar ta ce dole ne a miƙa dukkan takardun kafin ƙarfe 5:00 na yamma ranar Juma’a, 21 ga Agusta, 2026, ta hanyar tashar yanar gizo ta hukuma kawai.
Kwamitin ya ce ana buƙatar yin nazari mai zurfi kan batutuwa kamar samun kuɗaɗen gudanarwa masu ɗorewa, tsarin umarni da kula da ayyukan ’yan sanda, ƙa’idojin ɗaukar ma’aikata da horar da su, iyakokin ikon aiki, haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, hanyoyin tabbatar da alhaki, da kuma matakan hana tsoma bakin siyasa ko cin zarafin iko.
Ya ce waɗannan batutuwa sun nuna muhimmancin samun kyakkyawar tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin samar da tsarin ’yan sanda mai inganci, gaskiya, ɗorewa da kuma amsa buƙatun tsaro na al’ummomi daban-daban a faɗin ƙasar.
A ƙarshen aikinsa, Kwamitin Aiki na Shugaban Ƙasa zai gabatar da cikakkiyar daftarin Dokar ‘Yan Sanda ta Ƙasa wadda za ta kasance a shirye domin aiwatarwa, domin ci gaba da tsarin gabatar da ita ga majalisar dokoki.
Kwamitin ya gode wa masu ruwa da tsaki da suka riga suka gabatar da ra’ayoyinsu, tare da ƙarfafa gwiwar sauran waɗanda ke son shiga cikin wannan muhimmin tsari na ƙasa da su yi amfani da ƙarin lokacin da aka bayar.