Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya reshen Jihar Gombe, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ASF MB Mu’azu, ya sanya wa hannu a ranar Juma’a.


A cewar sanarwar, “rundunar ta samu kiran gaggawa game da lamarin da ƙarfe 3:03 na rana, sannan ta tura motar kashe gobara mai ɗauke da ruwa mai lamba FFS 215 Multipurpose Water Tender daga tashar kashe gobara ta ATM, bayan mintuna biyar.”


Ta ce jami’an kashe gobara sun isa wurin da misalin 3:15 na rana, inda suka tarar da gobarar ta kama gidaje biyu waɗanda suka ƙunshi ɗakuna da dama.


Sanarwar ta ce, “nan take ma’aikatan suka fara aikin kashe gobarar, kuma daga ƙarshe suka samu nasarar kashe ta ta hanyar amfani da matsakaicin bututun feshi da aka haɗa da tankin ruwan motar.”


Ta ƙara da cewa, matakin gaggawar da jami’an kashe gobarar suka ɗauka ya hana gobarar yaɗuwa zuwa wasu wurare, tare da taimakawa wajen ceto dukiya da aka kiyasta darajarta da Naira miliyan 150.


Sanarwar ta ce, “Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, Rundunar Jihar Gombe, ta samu nasarar shawo kan wata gobara da ta tashi a gidajen zama guda biyu da ke Yalenguruza Quarters, daura da MacConnels Hotel, a Jihar Gombe.”