An saki wani Ba’amurke mai aikin mishan, Kevin Rideout, wanda aka yi garkuwa da shi a Nijar kusan watanni 10 da suka gabata, bayan ya shafe dogon lokaci a hannun masu garkuwa da mutane.

Ƙungiyar mishan ta Serving In Mission (SIM) ta tabbatar da sakin Rideout, tana mai cewa yana cikin ƙoshin lafiya kuma yanzu yana hannun jami’an gwamnatin Amurka.

Garkuwa da Rideout ta jawo hankalin ƙasashen duniya tare da haifar da wani gagarumin bincike domin gano inda yake a yankin Sahel.

Iyalansa sun bayyana matuƙar godiya ga jama’a bisa addu’o’i da goyon bayan da suka nuna musu tun bayan sace shi.

Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan yadda aka sako shi ko kuma waɗanda suka yi garkuwa da shi ba.

An yi garkuwa da Rideout, wanda ke aikin agaji da wa’azin Kiristanci, a gidansa da ke Yamai, babban birnin Nijar, a watan Oktoban bara.

Ana kyautata zaton cewa wasu mayaƙa masu iƙirarin jihadi da ke aiki a yankin Sahel ne suka yi garkuwa da shi.

Yankin Sahel na daga cikin yankunan duniya da ke fama da matsanancin rashin tsaro da hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.