Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da hukumomin tsaro da su tabbatar da gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Osun cikin zaman lafiya, gaskiya da sahihanci.
Al’ummar Jihar Osun za su je rumfunan zaɓe a yau, Asabar 15 ga Agusta, 2026, domin zaɓen gwamna, inda ’yan takara 15 ke neman kujerar gwamnan jihar.
Daga cikin ’yan takarar akwai Gwamna mai ci, Ademola Adeleke, ɗan takarar APC, Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji, da ɗan takarar ADC, Najeem Salaam.
A cikin wata sanarwa da Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya buƙaci masu zaɓe a Osun su fito su gudanar da haƙƙinsu na ɗan ƙasa, tare da guje wa duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiyar zaɓen.
Shugaban ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron jama’a kafin, lokacin da kuma bayan zaɓen.
Tinubu ya ce INEC ya kamata ta yi amfani da wannan zaɓen da ba ya gudana tare da sauran zaɓuka a matsayin gwajin ƙarshe da zai nuna wa ’yan Najeriya irin shirye-shiryen da hukumar ta yi gabanin babban zaɓen 2027.
Ya kuma umarci Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya da sauran shugabannin hukumomin tsaro da za su shiga aikin tabbatar da tsaron zaɓen da su samar da cikakken tsaro a rumfunan zaɓe.
Shugaban ya jaddada cewa ba za a bari masu tayar da hankali su kawo cikas ga tsarin zaɓen ba, tare da tabbatar da cewa jami’an zaɓe da masu kaɗa ƙuri’a za su samu kariya domin gudanar da ayyukansu ba tare da tsoro ko tsoratarwa ba.
Sanarwar ta ƙarfafa wa masu zaɓe gwiwa da su fito da yawa domin zaɓar ɗan takarar da suke so, tana mai cewa an ɗauki dukkan matakan da suka dace domin gudanar da zaɓe cikin lumana, ’yanci da adalci.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa dole ne zaɓe ya kasance abin dogaro, kuma sakamakon zaɓen gwamnan Osun ya kamata ya nuna ainihin muradin al’ummar jihar.