Al'ummar garin Lakwaya da ke Karamar Hukumar Gwarzo a Jihar Kano sun

kwana cikin zullumi bayan harin da 'yan bindiga suka kai garin a daren Juma'a.


Bayanai daga mazauna garin da dama

sun zargi cewa 'yan bindigar sun shiga Lakwaya, inda suka harbi mutane tare da yin garkuwa da wasu da kuma korar shanu.


Huzaifa Ibrahim Lakwaya ya bayyana

cewa, 'yan bindigar sun harbi mutane biyu, sun yi garkuwa da mutane biyu tare da korar shanu, yayin da Couch Figo Lakwaya ya tabbatar da harbin mutane biyun, yana mai cewa daya an harbe shi a hannu, daya kuma a fuska, sannan ya ce an tafi da wasu mutane da bai san adadinsu ba.


Gambo Yuseef Lakwaya ya bayyana cewa, harin ya same su suna cikin aji a makaranta, inda ya ce 'yan bindigar sun saita masa bindiga tare da neman kudi ko waya, yayin da Aminu Usman Apply Lakwaya ya ce harin ya firgita jama'ar garin.