Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce Najeriya na cikin kasashen da aka samu rahotannin kai hare-hare kan jami'an lafiya da cibiyoyin kiwon lafiya.
WHO ta ce an tabbatar da sama da
hare-hare 10,000 kan harkokin lafiya tun daga shekarar 2018 zuwa yanzu, a kasashe da yankuna 29.
Hare-haren sun yi sanadin mutuwar
kusan mutum 5,700 tare da jikkata wasu 8,500, amma WHO ta ce kawo yanzu ba a gurfanar da kowa a gaban hukuma kan wadannan hare-hare ba.
Altaf Musani, daraktan sashen agaji da kula da bala'o'i na WHO, ya bayyana alaluman a wani taron manema labarai a Geneva.
Ya ce cibiyoyin lafiya da tsarin kiwon
lafiya na karkashin kariyar dokokin kasa da kasa, musamman dokokin jinkai da hakkin dan Adam da yarjejeniyar Geneva ta tanada.
Sai dai ya ce duk da sama da hare-hare
10,000 da WHO ta tabbatar, "babu ko guda daya da ya shiga tsarin da zai kai ga hukunta masu aikata su."
A bana kadai, WHO ta ce ta tabbatar da
hare-hare 914, wadanda suka kashe mutum 911 tare da jikkata 1,486. kai hare-hare kan jami'an lafiya da cibiyoyin kiwon lafiya.
WHO ta ce an tabbatar da sama da
hare-hare 10,000 kan harkokin lafiya tun daga shekarar 2018 zuwa yanzu, a kasashe da yankuna 29.
Hare-haren sun yi sanadin mutuwar
kusan mutum 5,700 tare da jikkata wasu 8,500, amma WHO ta ce kawo yanzu ba a gurfanar da kowa a gaban hukuma kan wadannan hare-hare ba.
Altaf Musani, daraktan sashen agaji da kula da bala'o'i na WHO, ya bayyana alaluman a wani taron manema labarai a Geneva.
Ya ce cibiyoyin lafiya da tsarin kiwon
lafiya na karkashin kariyar dokokin kasa da kasa, musamman dokokin jinkai da hakkin dan Adam da yarjejeniyar Geneva ta tanada.
Sai dai ya ce duk da sama da hare-hare
10,000 da WHO ta tabbatar, "babu ko guda daya da ya shiga tsarin da zai kai ga hukunta masu aikata su."
A bana kadai, WHO ta ce ta tabbatar da
hare-hare 914, wadanda suka kashe mutum 911 tare da jikkata 1,486.