Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarun Operation FANSAN YAMMA sun kashe ’yan ta’adda biyu tare da kwato bindigogi, alburusai da babura yayin wani samame a yankin Garin Kaso, ƙaramar hukumar Birnin Magaji ta jihar Zamfara.

A cewar sanarwar da rundunar ta fitar, dakarun sun yi artabu mai tsanani da ’yan ta’addan a ranar Juma’a, 14 ga Agusta 2026, inda suka kwato bindigogi biyu, magazina biyu, harsasai tara da babura biyu.

Rundunar ta ce daga bisani wasu ’yan ta’adda sun yi ƙoƙarin yi wa sojojin kwanton bauna daga maɓoyarsu, amma dakarun sun yi nasarar fatattakar su tare da jikkata wasu daga cikinsu, lamarin da ya tilasta wa sauran tserewa.

Sojojin sun kuma ce ba a tabbatar da adadin waɗanda suka mutu a artabun na biyu ba, sai dai rahotannin al’ummomin yankin sun nuna cewa wasu daga cikin ’yan ta’addan da suka jikkata da gawarwakin waɗanda aka kashe an kwashe su daga wurin.

A wani samame na daban, dakarun sun kama wani mutum mai suna Sani Umar, mai shekaru 57, da ake zargi da safarar abubuwan fashewa. An gano guda 180 na 20mm Super Power explosives a cikin motarsa yayin binciken ababen hawa a ƙaramar hukumar Gusau.

Rundunar ta ce ana zargin an yi niyyar kai kayan zuwa ga ’yan ta’adda da ke aiki a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina. An tsare wanda ake zargin, motarsa da kayan fashewar domin ci gaba da bincike.