Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Nuru Khalid, ya ce a wasu lokuta suna fuskantar ƙalubalen samun damar ganawa da shugaban ƙungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa'iqamatis Sunnah, Sheikh Sani Yahaya Jingir, domin tattaunawa da ba shi shawara kan wasu batutuwa da suka shafi addini da al'umma.

Sheikh Nuru Khalid ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa, inda ya yi bayani kan dangantakar da ke tsakanin malaman addinin Musulunci da yadda suke mu'amala da juna duk da bambance-bambancen ra'ayi da ke iya kasancewa a tsakaninsu.

Ya ce a matsayinsu na malamai, ya kamata su riƙa tattaunawa da juna tare da ba da shawarwari idan sun ga akwai wasu batutuwa da suka dace a gyara ko a yi karin bayani a kansu.

Sai dai Sheikh Nuru Khalid ya ce ba a ko da yaushe suke samun damar isar da irin waɗannan shawarwari ga Sheikh Sani Yahaya Jingir ba.

Malamin ya jaddada muhimmancin haɗin kai, fahimtar juna da tattaunawa tsakanin malaman addini, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen ciyar da al'umma gaba tare da rage yiwuwar rikice-rikicen da ka iya tasowa sakamakon bambancin fahimta.

Ana iya kallon cikakkiyar tattaunawar a shafin BBC Hausa na Facebook.