Fitacciyar jarumar fina-finan Amurka, Hayden Panettiere, wadda ta yi fice a shirye-shiryen talabijin na Heroes da Nashville, ta rasu tana da shekara 36. Iyalanta ne suka tabbatar da rasuwar ta hannun wakilinta.

Mahaifinta, Skip Panettiere, ya bayyana ta a matsayin mutum mai matuƙar kawo farin ciki da ƙauna ga iyalanta da kuma miliyoyin mutanen da suka san ta ta hanyar fina-finai.

Panettiere, wadda aka haifa a shekarar 1989, ta fara sana’ar fim tun tana ƙarama, kafin ta samu karɓuwa sosai sakamakon rawar da ta taka a Heroes da Nashville. Ta kuma fito a fina-finai irin su Remember the Titans, Ice Princess, Scream 4 da Scream VI.

A farkon shekarar 2026, Panettiere ta wallafa littafin tarihin rayuwarta mai suna This Is Me: A Reckoning, inda ta bayyana wasu daga cikin ƙalubalen da ta fuskanta a rayuwarta, ciki har da matsalar shaye-shaye da kuma yadda ta yi ƙoƙarin murmurewa.

A halin yanzu, ba a bayyana musabbabin rasuwarta a hukumance ba, yayin da bincike kan lamarin ke ci gaba.