Sarkin Gumel da ke Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Muhammad Sani, ya rasu bayan shafe shekara 46 yana kan karagar mulkin masarautar.

Sakataren Masarautar Gumel, Alhaji Murtala Aliyu, ne ya tabbatar wa BBC rasuwar sarkin a yau Alhamis, a birnin Alƙahira na ƙasar Masar.

A cewar sakataren masarautar, marigayin ya shafe kusan makonni shida yana jinya a wani asibiti da ke Alƙahira kafin rasuwarsa.

Sarkin ya kasance ɗaya daga cikin sarakunan arewacin Najeriya da suka fi dadewa a kan karagar mulki. Sakataren masarautar ya ce marigayin shi ne sarki na 16 a jerin sarakunan Masarautar Gumel, kuma shi ne sarkin da ya fi kowa dadewa a kan gadon sarautar masarautar.

Ya ƙara da cewa nan gaba ne za a dawo da gawar marigayin gida domin gudanar da shirye-shiryen jana'izarsa.

Sarkin ya rasu ya bar matan aure uku da ’ya’ya sama da 30.

Sakataren Masarautar Gumel ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai haƙuri, mai son zumunci, kuma mai matuƙar ƙaunar al’ummarsa.

An haifi Ahmed Muhammad Sani a shekarar 1939 a garin Gumel, da ke Jihar Jigawa a yanzu.

A watan Disamban 1980 ne aka naɗa shi Sarkin Gumel, bayan rasuwar mahaifinsa, marigayi Muhammad Sani, wanda shi ma ya kasance tsohon Sarkin Gumel.