Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya jagoranci taron Majalisar Tsaro ta Jihar a ranar Laraba, domin duba halin tsaro a jihar, yayin da rundunar ’yan sanda ta tabbatar da kama wasu da ake zargi da hannu a hare-haren baya-bayan nan.

An gudanar da taron ne a Sabon Gidan Gwamnati da ke Little Rayfield, Jos, a daidai lokacin da wasu al’ummomin jihar ke fuskantar hare-hare.

Tattaunawar ta mayar da hankali kan sabbin barazanar tsaro, hare-haren da suka faru kwanan nan, tattarawa da musayar bayanan sirri, matakan kariya, haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, da hanyoyin kare rayuka da dukiyoyi tare da tabbatar da ci gaban harkokin tattalin arziki a faɗin jihar.

Da yake magana bayan taron, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Plateau, CP Ayodeji Faniyan, ya ce an kama wasu mutane da ake zargi da hannu a wasu daga cikin manyan hare-haren da suka faru a jihar a cikin watan da ya gabata.

Kwamishinan ya ce bincike na ci gaba da gudana domin gano tare da cafke sauran waɗanda ake zargi da hannu a hare-haren.

Ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro za su ci gaba da aiki tare domin ƙarfafa matakan tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.