Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce yana da yaƙinin cewa gwamnatin Iran za ta ruguje nan ba da jimawa ba.

Netanyahu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wani taro da manyan jami’an sojin Isra’ila suka halarta, inda ya ce gwamnatin Iran na cikin wani yanayi na rauni fiye da kowane lokaci.

“Yanzu gwamnatin Iran na cikin wani yanayi mai matuƙar rauni. Ta fi kowane lokaci a baya rauni, kuma tana ƙoƙarin tabbatar da kanta ne kawai,” in ji shi.

Firaministan Isra’ilan ya ƙara da cewa yana da yaƙinin cewa za a iya kawar da abin da ya kira barazanar Iran gaba ɗaya, tare da kawo ƙarshen gwamnatin ƙasar.

“Wannan shi ne babban aiki mafi muhimmanci da har yanzu ke gabanmu. Muna ƙara matsowa kusa da cimma hakan. Ba abu ne mai wuya ba, kuma abu ne da za mu iya yi,” in ji Netanyahu.

Netanyahu ya kuma yi magana kan hare-haren da Iran ke kaiwa a cikin yaƙin da take yi da Amurka, inda ya ce rashin kai wa Isra’ila hari ba da gangan ba ne.

“Ba da gangan ba ne ba sa kai mana hari. Suna kai wa kowa hari, amma ba sa kai mana hari saboda sun san ƙarfinmu,” in ji shi.

Kalaman na Netanyahu sun zo ne a daidai lokacin da Isra’ila ke shirin gudanar da babban zaɓe a ranar 27 ga Oktoba, yayin da wasu ƙuri’un jin ra’ayin jama’a ke nuna cewa yana fuskantar ƙalubale daga jam’iyyun adawa.

Shugabannin ‘yan adawar Isra’ila na zargin Netanyahu da gaza magance batun Iran yadda ya kamata, lamarin da suka ce na iya shafar matsayinsa a siyasa.