Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da sabuwar ƙarar Naira biliyan 10 a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin hukumar ICPC ta hana shi ganin iyalansa yayin da take tsare da shi.
El-Rufai, ta hannun lauyansa Ubong Akpan, ya shigar da ƙarar ne a ranar 13 ga Agustan 2026. Ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1852/2026 ta ƙunshi buƙatu guda tara, ciki har da neman kotu ta tabbatar da cewa haƙƙoƙinsa na asali da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada suna nan daram duk da cewa yana tsare.
Tsohon gwamnan ya zargi ICPC da hana matarsa, Aichatou Asabe, da ɗansa, Abba El-Rufai, ziyartarsa da kuma kai masa abinci, magunguna, tufafi da sauran abubuwan da yake buƙata yayin da yake tsare.
El-Rufai ya ce wannan mataki ya tauye masa haƙƙoƙinsa, yana kuma neman kotu ta umarci hukumar da ta ba shi damar yin hulɗa cikin sauƙi da iyalansa da lauyoyinsa yayin tsarewar.
Ya kuma nemi a biya shi Naira biliyan 10 a matsayin diyya kan abin da ya bayyana a matsayin take haƙƙinsa na ɗan Adam.
Rahotanni sun ce ƙarar ta zo ne a cikin jerin matakan shari'a da El-Rufai ke ɗauka kan yadda ICPC ke gudanar da bincike da tsare shi.