Mamakon ruwan sama da aka yi a Abuja ya haddasa ambaliyar ruwa a wasu sassan Babban Birnin Tarayya, lamarin da ya jefa mazauna yankunan cikin halin ƙunci tare da kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa.
Daga cikin wuraren da ambaliyar ta fi shafa akwai Wuse 2, musamman titin Adetokunbo Ademola, inda ruwa ya mamaye hanyoyi da wasu gidaje.
Bidiyoyin da suka yaɗu a kafafen sada zumunta sun nuna yadda motoci da dama suka makale ko kuma suka nutse cikin ruwan ambaliya, yayin da direbobi da fasinjoji suka kasa ci gaba da tafiya.

Ambaliyar ta kuma shafi yankunan Gudu, Maitama, Lokogoma da hanyar da ta haɗa Gaduwa da Durumi, inda ruwa ya mamaye wata gada tare da katse zirga-zirga.
Wasu ’yan kasuwa sun rufe shagunan su bayan ruwa ya shiga wuraren kasuwancinsu, yayin da mazauna yankunan suka yi kira ga hukumomi da su ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalar.
Lamarin ya sake jawo hankali kan matsalar magudanan ruwa a Abuja, musamman ganin cewa hukumomin hasashen yanayi sun yi gargaɗin yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wasu sassan birnin a bana.