Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta kama wata matashiya mai shekaru 19, Khadija Ibrahim, bisa zargin satar wani jariri da aka haifa a Zuru tare da kai shi wajen mijinta, tana mai cewa ɗansu ne.
A cewar rundunar, lamarin ya faru ne a ranar 23 ga Yuli, 2025, jim kaɗan bayan mahaifiyar jaririn, Fatima Muhammad, ta haife shi.
Ana zargin Khadija ta nemi taimakawa sabuwar mahaifiyar wajen samo mata ruwan zafi, amma ta yi amfani da damar wajen ɗauke jaririn tare da guduwa da shi.
Binciken ’yan sanda ya nuna cewa ana zargin matashiyar ta fuskanci matsin lamba na zamantakewa da na tunani sakamakon rashin haihuwa, musamman ganin yadda wasu daga cikin ƙawayenta suka riga suka samu ’ya’ya.
Haka kuma, ana zargin Khadija da yaudarar mijinta na kusan watanni tara, inda ta sa shi ya yi imanin cewa tana da juna biyu. Bayan satar jaririn, sai ta kai shi gare shi tana mai gabatar da shi a matsayin ɗansu.
Rundunar ta ce daga bisani jami’anta sun gano jaririn tare da mayar da shi ga mahaifiyarsa, kuma yana cikin ƙoshin lafiya.
A halin yanzu, Khadija na hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kafin gurfanar da ita a gaban kotu.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kebbi, CP Umar Hadejia, ya yabawa jami’an rundunar bisa gano jaririn da kuma kama wadda ake zargin, yana mai tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare yara tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen aikata laifi.