Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar kai wa Oman hare-haren bama-bamai idan ta “tsoma baki” ko ta kawo cikas ga ƙoƙarin Amurka kan yadda za a buɗe mashigar ruwan Hormuz a cikin rikicin da take yi da Iran.

Trump ya yi wannan gargaɗin ne a wata tattaunawa da gidan talabijin na Fox News ranar Litinin, yayin da Iran da Oman ke ƙoƙarin cimma matsaya kan tsarin da jiragen ruwa za su bi wajen ratsa mashigar.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta ce Tehran da Muscat sun cimma matsaya kan taswirar hanyar da jiragen ruwa za su bi, yayin da ake ci gaba da kammala sauran bayanai kafin sanar da yarjejeniyar a hukumance.

Rahotanni sun ce Oman na nazarin tattaunawar da kyakkyawar niyya, yayin da Amurka ke matsa lamba kan a sake buɗe mashigar Hormuz gaba ɗaya domin zirga-zirgar kasuwanci.

A cikin hirar, Trump ya kuma ce Amurka na da hanyar sadarwa kai tsaye da jami’an Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran, IRGC, sai dai daga baya rahotanni suka ce IRGC ta musanta cewa tana tattaunawa da Amurka.

A gefe guda, Iran ta ce tana dab da kammala yarjejeniya da Oman kan yadda za a gudanar da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz, wadda ke da matuƙar muhimmanci ga jigilar man fetur da iskar gas a duniya.

Batun sake buɗe mashigar Hormuz na daga cikin manyan batutuwan da ke gaban Amurka da Iran yayin da ƙoƙarin cimma yarjejeniyar dakatar da rikicin tsakanin ƙasashen ke fuskantar tsaiko.