Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Bauchi (BASIEC) ta bayyana cewa APM ta kuma lashe kujerun kansiloli 319 daga cikin 323.


Shugabar hukumar, Jummai Abubakar, ta ce dukkan ‘yan takarar APM 20 sun samu nasara bayan kammala kada kuri’a, kirga kuri’u da tattara sakamako.


Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya soki jam’iyyun adawa kan kaurace wa zaben, yana mai cewa sun yi hakan ne saboda tsoron faduwa.


Gwamnan ya bayyana zaben a matsayin wanda aka gudanar cikin kwanciyar hankali, tare da jaddada muhimmancin kananan hukumomi wajen samar da ci gaba da kyakkyawan shugabanci.