Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), ta ce sama da malaman jami’a 200, ciki har da masu muƙamin farfesa, sun bar jami’ar sakamakon abin da ta bayyana a matsayin rashin ingancin tsarin gudanarwa da kuma gazawar aiwatar da yarjejeniyar Gwamnatin Tarayya da ASUU ta shekarar 2025.
Shugaban ASUU-KASU, Abubakar Abdullahi, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata hira da manema labarai a sakatariyar ƙungiyar da ke cikin harabar jami’ar a Kaduna.
Abdullahi ya ce yarjejeniyar FGN-ASUU, wadda ta tanadi inganta yanayin aiki da jin daɗin malaman jami’o’in Najeriya, ta fara aiki tun daga watan Janairun 2026, amma har yanzu ba a fara aiwatar da ita a KASU ba.
Ya ce wannan yanayi ya jefa malaman jami’ar cikin damuwa, tare da haddasa ficewar dimbin malamai daga jami’ar.
Shugaban ASUU-KASU ya ce ƙungiyar ta rubuta wasiƙu da dama ga hukumar gudanarwar jami’ar, Majalisar Shugabanci da kuma shugaban jami’ar, tare da tura koke ga Gwamnan Jihar Kaduna, domin neman a tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.
ASUU-KASU ta kuma bai wa hukumomin jami’ar da sauran masu ruwa da tsaki wa’adin makonni biyu da su fara aiwatar da yarjejeniyar, tana mai gargadin cewa rashin yin hakan na iya tilasta mata ɗaukar matakin yajin aikin sai baba-ta-gani a jami’ar.
Abdullahi ya ce ƙungiyar ba ta son rikici, amma za ta ɗauki matakan da suka dace domin kare haƙƙin malaman jami’ar da kuma tabbatar da ingantaccen yanayin aiki.