Majalisar Ɗinkin Duniya, MDD, ta ce kashi 40 cikin 100 na cibiyoyin kiwon lafiya a duniya ne kawai ke da muhimman ayyukan tsaftar muhalli, ciki har da ingantattun bandakuna.

Wani sabon rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, da UNICEF suka fitar ya nuna cewa kashi 11 cikin 100 na cibiyoyin kiwon lafiya ba su da wata hidimar tsafta kwata-kwata, lamarin da ke shafar kusan mutane miliyan 936 a duniya.

Rahoton ya kuma nuna babban gibi tsakanin yankuna, inda kashi 23 cikin 100 na cibiyoyin kiwon lafiya a yankin Afirka ta Kudu da Sahara ke da ingantattun ayyukan tsafta, idan aka kwatanta da kashi 55 cikin 100 a Tsakiya da Kudancin Asiya.

Baya ga tsafta, rahoton ya ce kashi 85 cikin 100 na cibiyoyin kiwon lafiya a duniya suna da muhimman ayyukan samar da ruwa, yayin da kashi 59 cikin 100 kawai ke da ingantattun ayyukan tsaftace muhalli.

Rahoton WHO da UNICEF, wanda ya duba bayanan shekarar 2025, ya ce rashin wadatattun kayan tsafta da ruwa a cibiyoyin kiwon lafiya na iya ƙara haɗarin yaɗuwar cututtuka tare da jefa marasa lafiya da ma’aikatan lafiya cikin barazana.