Kakakin Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya sake jaddada cewa Iran ba za ta buɗe Mashigar Hormuz ba har sai Amurka ta cika dukkan sharuɗɗan da ke cikin yarjejeniyar wucin gadi da aka cimma tsakanin ƙasashen biyu.

Qalibaf ya ce daga cikin sharuddan akwai ɗage takunkuman da aka kakaba wa Iran, sakin kadarorin ƙasar da aka daskarar, kawo ƙarshen takunkumin da ya shafi man fetur da kuma dakatar da duk wata barazanar soja ko farmaki kan Iran.

Ya kuma yi gargaɗin cewa Iran a shirye take ta mayar da martani mai tsanani idan aka sake kai mata hari, yayin da jami’an ƙasar ke ƙara matsa kaimi kan matsayinsu game da makomar mashigar.

Kalaman na Qalibaf sun zo ne yayin da wa’adin kwanaki 60 da aka tanada a yarjejeniyar wucin gadi tsakanin Amurka da Iran ya ƙare ba tare da an cimma cikakkiyar yarjejeniya ba. Amurka ta ce ba za ta tsawaita yarjejeniyar ba, yayin da Tehran ke zargin Washington da rashin cika nata ɓangaren na yarjejeniyar.

Mashigar Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin safarar man fetur da iskar gas a duniya, kuma takaddamar da ke tsakaninsu ta riga ta haifar da raguwar zirga-zirgar jiragen ruwa tare da ƙara fargabar hauhawar farashin makamashi a duniya.