Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta gurfanar da wani mutum mai suna Lawal Babale Musa a gaban Babbar Kotun Jihar Oyo da ke Ibadan, bisa zargin damfarar wasu maniyyatan aikin Hajji kuɗi har Naira miliyan 56.49.
EFCC ta gurfanar da Musa kan tuhume-tuhume 57 da suka shafi zargin sata, jabun takardu da kuma amfani da takardun bogi.
Hukumar ta ce mutum 10 na daga cikin waɗanda ake zargin Musa ya karɓi kuɗaɗensu, inda jimillar kuɗin da ake zargin ya karɓa ta kai N56,491,000 tsakanin watan Nuwamban 2022 da Yulin 2024.
A cewar EFCC, Musa ya riƙa gabatar da kansa ga waɗanda ya karɓi kuɗin a wurinsu a matsayin jami’in da ke kula da aikin Hajji na Jihar Kaduna, tare da yi musu alƙawarin taimaka musu wajen shirya tafiyarsu zuwa aikin Hajjin shekarar 2023.
Hukumar ta ƙara da cewa wanda ake zargin ya ba wasu daga cikin maniyyatan rasitocin bogi da aka nuna cewa an bayar da su daga hukumomin Jihar Kaduna da kuma Saudiya, domin ya tabbatar musu cewa an karɓi kuɗaɗensu.
An gurfanar da Musa ne a gaban Mai Shari’a Olusola Adetujoye, yayin da kotun ke ci gaba da sauraron shari’ar da ta shafi zargin damfarar maniyyatan.