Wata babbar kasuwa mai suna SUFAYE Investment da ke Kano ta miƙa kayayyakin abinci da sauran kayayyakin da suka lalace ko suka ƙare wa’adin amfani da su, waɗanda darajarsu ta haura Naira miliyan 28, ga Majalisar Kare Hakkin Masu Sayayya ta Jihar Kano domin lalata su.
Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Majalisar, Jamilu Mustapha, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Kano.
Sakataren Zartarwa na Majalisar, Dr Ibrahim Garba-Muhammad, ya bayyana matakin da kamfanin ya ɗauka a matsayin abin a yaba, yana mai kira ga sauran kamfanoni da ’yan kasuwa a jihar da su yi koyi da SUFAYE wajen cire kayayyakin da suka lalace ko suka gurɓata daga kasuwa, maimakon sayar da su ga jama’a.
Ya yaba wa mazauna jihar, kamfanoni da ’yan kasuwa bisa haɗin kai da goyon bayan da suke bai wa Majalisar wajen kare lafiyar masu sayayya da tabbatar da inganci da tsaron kayayyakin da ake sayarwa a kasuwa.
Manajan SUFAYE Investment, Alhaji Jabir, ya ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin kamfanin na tabbatar da cewa kayayyakin da suka lalace ko suka ƙare wa’adinsu ba su isa hannun kwastomomi ba.
Ya ce mahukuntan kamfanin na gudanar da bincike akai-akai kan kayayyakin da suke da su domin tabbatar da bin ƙa’idojin hukumomin da abin ya shafa da kuma ingantattun hanyoyin kasuwanci.
Jabir ya kuma yaba wa Majalisar Kare Hakkin Masu Sayayya ta Kano bisa ci gaba da sa ido da duba kayayyakin da ake sayarwa a kasuwa, yana mai cewa hakan na taimakawa matuƙa wajen kare lafiyar jama’a.
Ya tabbatar da cewa kamfanin zai ci gaba da samar da kayayyaki masu inganci, musamman abubuwan sha, tare da bayar da gudunmawa wajen bunƙasa tattalin arzikin Jihar Kano.