Ministan Kuɗi kuma Mai Gudanar da Tattalin Arziƙin Najeriya, Taiwo Oyedele, ya ce gyare-gyaren tattalin arzikin da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa sun taimaka wajen ƙara yawan kuɗaɗen da ake rabawa jihohi da ƙananan hukumomi duk wata zuwa sama da Naira tiriliyan biyu.
Oyedele ya ce adadin ya ƙaru daga matsakaicin Naira biliyan 300 da ake rabawa a ƙarƙashin gwamnatocin da suka gabata.
Ministan ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Owerri, Jihar Imo, yayin da yake buɗe taron nazari na Majalisar Ƙasa kan Kuɗi da Ci gaban Tattalin Arziƙi na shekarar 2026.
Ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnati ta aiwatar sun taimaka wajen ƙara yawan kuɗaɗen shiga da ake rabawa ta Asusun Rarraba Kuɗaɗen Tarayya (FAAC), wanda hakan ke bai wa jihohi da ƙananan hukumomi ƙarin damar gudanar da ayyukan ci gaba.
Oyedele ya bayyana cewa ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren tattalin arzikin na da muhimmanci wajen samar da ingantaccen tsarin tattalin arziki da zai ƙara bunƙasa kuɗaɗen shiga da kuma inganta rayuwar ’yan Najeriya.