Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta ce jami’anta sun kwace kilogiram 184.5 na hodar Iblis (cocaine) daga wani kamfanin aika kaya da ke Legas.

Hukumar ta bayyana kwacen a matsayin mafi girman hodar Iblis da ta taɓa kwacewa daga kamfanin aika kaya tun bayan kafuwarta.

Shugaban NDLEA, Buba Marwa, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Legas ranar Talata.

Marwa ya ce jami’an hukumar sun kama mutane biyu da ake zargi da hannu wajen safarar wannan muggan ƙwayoyi.

Hukumar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken tsarin safarar hodar Iblis ɗin da kuma sauran mutanen da ka iya kasancewa da hannu a lamarin.