Jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta lashe dukkan kujerun shugabancin ƙananan hukumomi 20 a zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a faɗin Jihar Bauchi ranar Litinin.

Shugabar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Bauchi (BSIEC), Jummai Abubakar, ce ta bayyana sakamakon zaɓen.

Ta ce baya ga kujerun shugabancin ƙananan hukumomi 20, jam’iyyar APM ta kuma lashe kujerun kansiloli 319 daga cikin 323 da aka fafata a jihar.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin jam’iyyun adawa sun kaurace wa zaɓen, lamarin da ya bai wa APM damar lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomin jihar.