Bankin Standard Chartered Nigeria Limited ya haɗa gwiwa da Junior Achievement Nigeria (JAN) domin faɗaɗa damar matasan Najeriya samun horon ƙwarewar fasahar zamani, ta hanyar wani shiri na musamman mai suna Digital Bootcamp Program.
Shirin na da nufin shirya matasa domin su samu ƙwarewar da ake buƙata a kasuwar aikin zamani da tattalin arzikin da ke ƙara dogaro da fasahar dijital.
A cewar sanarwar, za a horas da matasa sama da 600 a jihohin Ondo, Abuja, Rivers da Kaduna.
Za a gudanar da horon na tsawon kwanaki 10, inda mahalarta za su samu horo na aikace-aikace kan fannoni daban-daban da suka haɗa da:
- Gudanar da ayyuka (Project Management)
- Nazarin bayanai (Data Analysis)
- Tsaron yanar gizo (Cybersecurity)
- Tsarawa da inganta ƙwarewar masu amfani da manhajoji (UI/UX Design)
- Tallafin fasahar sadarwa (IT Support)
- Tallace-tallacen dijital (Digital Marketing)
Masu shirya shirin sun ce manufar haɗin gwiwar ita ce bai wa matasan Najeriya ƙwarewar da za ta taimaka musu wajen samun guraben aiki da kuma bunƙasa sana’o’insu a cikin tattalin arzikin dijital da ke saurin sauyawa.