Dakarun Sojin Najeriya sun kuɓutar da wata mata tare da ’ya’yanta biyu da ake zargin ’yan ta’adda ne suka yi garkuwa da su a shekarar 2017 a Jihar Borno.

Rahotanni sun ce an kuɓutar da su ne a yayin wani samame na bincike da dakarun suka gudanar a kusa da Gadar Amuda da ke jihar.

Wata kafar yaɗa labaran yaƙi da ta’addanci mai suna Zagazola Makama ta ruwaito cewa dakarun sun tare mutanen ne da misalin ƙarfe 6:30 na safe ranar 14 ga Agustan 2026, yayin da suke gudanar da sintiri a yankin.

An ce jami’an sun gano matar da ’ya’yanta biyu yayin sintirin, inda suka kuɓutar da su tare da kai su wurin da ya dace domin samun kulawa da taimakon da ya kamata.

Kuɓutar da su na zuwa ne a yayin da dakarun ke ƙara tsaurara sintiri da samamen share fagen ayyukan ’yan ta’adda a sassan Jihar Borno.