Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun dakile wani yunƙurin garkuwa da fararen hula da ’yan ta’adda suka yi a ƙauyen Unguwar Rogo da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara.
A yayin farmakin, sojojin sun kuɓutar da fararen hula tara, ciki har da wani jariri.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar haɗin gwiwar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 16 ga Agustan 2026, lokacin da wasu ’yan ta’adda, waɗanda ake zargin wani jagoransu mai suna Mallam Shuaibu ne, suka kai hari kan fararen hula da ke tafiya a wata hanyar cikin gida.
Sanarwar ta ce ana kyautata zaton harin na iya kasancewa ramuwar gayya ce kan kama wasu mutanen da ake zargi da haɗin gwiwa da ƙungiyar ’yan ta’addan.
Rahoton ya bayyana cewa ’yan ta’addan sun ɓuya ne a cikin gonar gero, inda suka buɗe wa motocin da ke wucewa wuta, lamarin da ya sa wasu direbobi suka rasa ikon sarrafa motocinsu.
Sai dai dakarun Sector 2 sun yi gaggawar mayar da martani, inda suka yi artabu da ’yan ta’addan tare da hana su damar aiwatar da garkuwar. Hakan ya tilasta wa maharan tserewa zuwa cikin dazuzzukan da ke kewaye da yankin.
Dakarun sun samu nasarar kuɓutar da fararen hula tara, ciki har da jariri, yayin da wasu mata biyu da suka samu raunukan harbin bindiga aka kwashe su zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.
Rundunar ta ce matan biyu na ci gaba da samun magani kuma suna ƙarƙashin kulawar jami’an lafiya.
Operation FANSAN YAMMA ta ce za ta ci gaba da matsa lamba kan ’yan ta’adda da kuma hana su samun damar kai hare-hare kan fararen hula, tare da ci gaba da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Arewa maso Yamma.