Jam’iyyu da ’yan takarar shugaban ƙasa a Najeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta farko a Abuja, yayin da ake shirye-shiryen fara yaƙin neman zaɓen shekarar 2027.

Yarjejeniyar ta ƙunshi alƙawarin gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin lumana, tare da kauce wa kalaman tunzura jama’a, tashin hankali da duk wani mataki da ka iya kawo cikas ga tsarin zaɓe.

Daga cikin ’yan takarar da suka halarci taron akwai Peter Obi na NDC, Donald Duke na PRP da Omoyele Sowore na African Action Congress (AAC).

Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Sanata Barau Jibrin, da wasu manyan ’yan siyasa sun halarci taron.

Sai dai Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar jam’iyyar APC, bai halarci taron ba. Haka kuma, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar ADC, Atiku Abubakar, bai samu halarta ba.

Da yake jawabi a wajen taron, Peter Obi ya ce bai kamata rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar ta zama wani bikin kawai ba.

Ya yi kira ga ’yan siyasa da su tabbatar da cewa halayensu da kalaman da suke amfani da su a lokacin yaƙin neman zaɓe da kuma bayan zaɓe sun yi daidai da abubuwan da suka yi alkawarin mutuntawa a cikin yarjejeniyar.