Ɗaliban Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zaria, za su wakilci Najeriya a gasar ƙirƙire-ƙirƙire ta jami’o’in duniya ta ENACTUS, wadda za a gudanar a birnin São Paulo na ƙasar Brazil a watan Nuwamba.
Tawagar ENACTUS ta ABU ta samu wannan damar ne bayan da ta lashe gasar ENACTUS ta ƙasa ta shekarar 2026, wadda aka gudanar a Legas daga ranar 11 zuwa 15 ga watan Agusta.
Gasar ta ƙasa ta haɗa ɗalibai daga jami’o’i da kwalejojin fasaha daban-daban daga sassan Najeriya, inda tawagar ABU ta yi nasara sakamakon wani aikin ƙirƙire-ƙirƙire da ta gabatar domin magance wasu daga cikin manyan matsalolin da ke addabar noman tumatur.
Aikin ya mayar da hankali ne kan magance matsalar ƙwarin da ke lalata tsirran tumatur kafin girbi, da kuma rage asarar amfanin gona bayan girbi.
Mai ba da shawara ga tawagar, Farfesa M.K. Aliyu, ya ce nasarar ɗaliban ta samo asali ne daga bincike mai zurfi, haɗin gwiwa da al’umma da kuma jajircewar ɗaliban wajen samar da mafita ga matsalolin da manoma ke fuskanta.
Yanzu tawagar ABU za ta fara shirye-shiryen wakiltar Najeriya a matakin duniya a São Paulo, inda za ta fafata da sauran jami’o’i daga ƙasashe daban-daban.