Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta da ke aiki a Arewa maso Yammacin ƙasar sun dakile wasu yunƙurin garkuwa da mutane da ’yan ta’adda suka yi a sassa daban-daban na Jihar Zamfara, tare da kuɓutar da fararen hula daga hannun maharan.
Rundunar ta ce a ranar 17 ga Agustan 2026, dakarunta sun kai ɗauki bayan samun rahoton sace mutane a kan hanyar Gurusu zuwa Anka.
Sojojin sun bi sahun maharan cikin gaggawa, lamarin da ya tilasta musu watsar da mutanen da suka yi garkuwa da su tare da tserewa zuwa cikin daji.
A yayin aikin, an samu nasarar kuɓutar da mutane bakwai, waɗanda suka haɗa da mata huɗu da yara uku, ba tare da sun samu wani rauni ba.
Haka kuma, a ƙaramar hukumar Tsafe, dakarun sun mayar da martani bayan samun bayanan sirri cewa wasu ’yan ta’adda na ƙoƙarin yin garkuwa da matafiya a kusa da ƙauyen Magazu.
Bayan musayar wuta tsakanin sojojin da maharan, ’yan ta’addan sun tsere zuwa cikin daji, yayin da dakarun suka kuɓutar da mutanen da suka yi garkuwa da su.
Rundunar ta ce wasu daga cikin waɗanda aka ceto sun samu raunukan harbin bindiga, inda aka garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci.
Sojin Najeriya sun tabbatar da cewa dakarunsu za su ci gaba da matsa lamba kan ’yan ta’adda tare da ƙara sintiri da ayyukan yaƙi da ta’addanci domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin Arewa maso Yamma.