Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya ta ce dakarunta sun ceto fasinjoji 22 da ’yan fashin teku suka yi garkuwa da su, tare da ƙwato wani jirgin ruwa na fasinja da aka sace a hanyar ruwa tsakanin Calabar da Ibaka a Jihar Akwa Ibom.

Rundunar ta ce an gudanar da aikin ceton ne bayan samun rahoton harin da aka kai wa jirgin a ranar 11 ga Agustan 2026.

A cewar Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar, Kyaftin Abiodun Folorunsho, maharan sun tare jirgin ne jim kaɗan bayan ya wuce yankin Enwang, inda suka yi awon gaba da jirgin tare da sace fasinjojin da ke cikinsa.

Ya ce jami’an FOB Ibaka, tare da haɗin gwiwar Operation Delta Safe da ’yan sandan ruwa, sun gudanar da wani samame domin gano mutanen da aka sace da kuma kwato jirgin.

Rundunar ta ce an kai fasinjojin da aka ceto asibitin FOB Ibaka domin gudanar da gwaje-gwajen lafiya da ba su agajin gaggawa.

Daga bisani, an mayar da fasinjojin zuwa Calabar tare da jirgin ruwan da aka kwato, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da tsaron hanyoyin ruwa a yankin.