Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta fara harkokin karatu a Kwalejin Fasaha ta Gaya Polytechnic nan ba da jimawa ba, yayin da ake ci gaba da aikin kafa makarantar.

Mai Taimaka wa Shugaban Kwamitin Aiwatar da Aikin Gaya Polytechnic, Suhailu Tijjani Khalil, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.

Sanarwar ta ce Shugaban Kwamitin, Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa, tare da Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Ali Haruna Makoda, da Sakataren Kwamitin, Shehu Sani Shehu, sun gana da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, inda suka gabatar masa da rahoton ci gaban aikin makarantar.

Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ya gabatar da cikakken bayani kan ayyukan da kwamitin ya gudanar, ci gaban da aka samu, ƙalubalen da ake fuskanta da kuma matakan da ake ɗauka domin kammala aikin.

A nasa ɓangaren, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen kammala sauran sassan aikin, domin tabbatar da fara harkokin karatu a makarantar cikin zangon karatun da ake ciki.

Gwamnatin ta ce kafa kwalejin na daga cikin matakan da ake ɗauka domin faɗaɗa damar samun ilimin fasaha da ƙwarewar sana’o’i ga matasa a Jihar Kano.