Ƙungiyar Tsofaffin Jami’an ’Yan Sandan Najeriya (NARPON), reshen Jihar Adamawa, ta yi alkawarin amfani da gogewarta wajen taimakawa wajen inganta tsaro da daƙile aikata laifuka a jihar.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na ’Yan Sanda shiyya ta 3, SP Aminu Umar Bashir, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.

Sanarwar ta ce Shugaban NARPON reshen Adamawa, ACP Dominic Yadubiya mai ritaya, ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci tawagar ƙungiyar zuwa ziyarar aiki a hedikwatar ’Yan Sanda ta shiyya ta 3 da ke Yola.

Yadubiya ya ce tsofaffin jami’an za su yi amfani da ƙwarewa da ilimin da suka samu a lokacin da suke aiki wajen taimakawa jami’an tsaro a fannoni daban-daban, ciki har da wayar da kan jama’a, hulɗa da al’umma, ba da shawarwari da daƙile aikata laifuka.

A nasa ɓangaren, Mataimakin Sufeton ’Yan Sanda mai kula da shiyya ta 3, AIG Osagie John Agans Irabor, ya yaba da matakin ƙungiyar, tare da buƙatar tsofaffin jami’an da su ci gaba da bayar da shawarwari da gudummawar da za ta taimaka wajen inganta aikin ’yan sanda.

Ya ce ƙwarewa da gogewar tsofaffin jami’an na da muhimmiyar rawa wajen taimaka wa jami’an da ke aiki wajen tunkarar kalubalen tsaro da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ’yan sanda da al’umma.